in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Boko Haram sun gudu zuwa Darack dake yankin tafkin Chadi
2014-10-16 10:06:48 cri

Bisa yunkurin rundunar sojojin Kamaru ta bangare guda da kuma sojojin Najeriya ta wani bangeren ta hanyar kai wani babban samame kansu, mayakan kungiyar Boko Haram ta Najeriya sun tsere a 'yan kwanakin baya bayan nan zuwa Darack, wani tsibirin tafkin Chadi dake kan iyaka tsakanin kasashen Kamaru da Nijeriya, domin su samu damar buya a kasar Chadi, in ji wata majiyar hukumomin tsaro.

Bisa luguden wuta ta sama da hare-haren kasa da muka kai kan su, haka zalika kuma tun lokacin da rundunar sojojin Najeriya ta dauki niyyar kai samame, yawancin mayakan bangaren abokin gaba suna neman ajiye makamai domin su ba da kansu, yayin da sauran suke neman gudu. Mun gani a ranar Litinin wani gungun Boko Haram da ya tsere zuwa Darack, in ji wannan majiya da ta fito daga jami'an tsaron kasar Kamaru. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China