in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kamaru ya bayyana kudurinsa na yaki da 'yan ta'dda
2014-10-14 10:49:48 cri

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya yabawa karfin halin mutanen nan 27, ciki har da Sinawa 10 da 'yan kasar ta Kamaru 17 da 'yan kungiyar Boko Haram suka sako ranar Asabar.

Sai dai duk da sakin wadannan mutane, shugaba Paul Biya ya nanata kudurin gwamnatinsa na kawar da masu tada kayar baya.

A jawabinsa, jakadan kasar Sin da ke Kamaru Wo Ruidi ya godewa shugaba Biya da dukkan bangarorin da abin ya shafa bisa kokarinsu na ganin an saki Sinawan da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya.

Jakadan na Sin ya ce, sakin Sinawan cikin nasara ya nuna irin kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Sin da Kamaru, ya kuma bayyana cewa, ta'addanci batu ne da ya gallabi duniya baki daya, kuma kasar Sin ta yi watsi da duk wani nau'i na ta'addanci, sannan a shirye take ta hada kai da dukkan kasashe, ciki har da Kamaru don yaki da ta'addanci.

Idan ba a manta ba, daga ranakun 16 da 17 ga watan Mayu, da kuma 27 ga watan Yuli ne mayakan Boko Haram suka sace wadannan mutane a arewacin kasar, ciki har da Sinawa 10, 'yan Kamaru 17, da kuma uwar gidan mataimakin firaministan kasar Amadou Ali. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China