in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana samun sabon tunani da canji kan tsarin tattalin arzikin kasar Sin
2014-10-21 16:53:04 cri

A jiya Litinin 20 ga wata ne aka bude cikakken zama karo na 4 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a nan birnin Beijing. Tun bayan kammala cikakken zaman karo na 3 na kwamitin zuwa karo na 4 wato shekara daya ke nan, an samu sabuwar alama kan tattalin arzikin kasar Sin. Kana tunanin gwamnatin kasar Sin kan wannan fanni ya canja daga dora muhimmanci kan dubawa zuwa sa ido, don haka aka sa kaimi ga jama'ar kasar da su kara kirkiro tare da kafa kamfanoni.

Game da canjin da aka samu kan tattalin arzikin kasar Sin a shekara daya da ta gabata, 'yan kasuwa sun shaida wannan ci gaba da aka samu kai tsaye. Shugaban sashen kula da harkokin saya da sayarwa na wani kamfanin aikin gona na lardin Hainan na kasar mai suna Wu Cheng ya bayyana cewa, yanzu hukumomin gwamnati suna mai da hankali sosai wajen gudanar da ayyuka bisa doka da ka'idoji, kuma wannan ya sa ya samu sauki wajen gudanar da ayyukan kamfaninsa. Wu Cheng ya ce,"Bayan da gwamnati ta fitar da ka'idoji 8, na ga an samu canji sosai. Mu da gwamnatin muna yin hadin gwiwa bisa ka'idojin da aka gindaya, kana gwamnati ta nuna goyon baya gare mu ta hanyar gabatar da wasu manufofi. Ina fatan gwamnatin za ta kara baiwa kamfanoni wasu iko a nan gaba."

'Yan kasuwa suna fatan gwamnati za ta kara ba su iko da kuma samar da yanayin ciniki cikin adalci, kuma ana kokarin cimma wannan buri ne tun daga shekarar 2013 har zuwa yanzu. A baya kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin shi ke da ikon duba manyan ayyukan kasar, Zhang Minglun, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin zuba jari na kwamitin ya bayyana cewa, suna kokarin duba yiyuwar mika ikon zuba jari ga kamfanoni a dukkan fannoni.

Yayin da ake kokarin mika iko ga kamfanoni, aikin yin kwaskwarima kan tsarin yin rajistar masana'antu da kamfanoni da aka fara gudanarwa a watan Maris na bana ya kawo sauki ga aikin yin rajistar kamfanoni. Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, ana kokarin samar da yanayin kafa kamfanonin da al'ummar kasar za su mallaka sannu a hankali. Li Keqiang ya ce, "A shekarar bana, mun yi kwaskwarima kan tsarin yin rajistar kamfanoni. Daga watan Janairu zuwa na Agusta, yawan sabbin kamfanonin da suka yi rajista ya zarce miliyan 8, wadanda suka samar da guraben aikin yi ga mutane fiye da miliyan 10. Tun lokacin da aka fara yin kwaskwarima kan tsarin yin rajistar kamfanoni zuwa yanzu wato kasa da rabin shekara, yawan sabbin kamfanonin da suka yi rajista ya karu da kashi 60 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Wasu sun siffanta wannan a matsayin karuwar da aka samu cikin sauri sosai, kuma ana samun yanayin kafa kamfanonin da al'ummar kasar ke mallaka sannu a hankali."

Ban da wannan kuma, an kyautata tsarin samun iznin shiga kasuwanni a muhimman fannoni a kasar Sin. Alal misali, kamfanin Sinopec mallakar gwamnatin kasar Sin ya yi kwaskwarima kan tsarinsa zuwa tsari irin na hadin gwiwa, inda aka shigar da kamfanoni masu zaman kansu cikin kasuwar sayar da man fetur. Wang Jun, mataimakin shugaban sashen nazari da ba da shawara na cibiyar yin mu'amalar tattalin arziki a tsakanin kasashen duniya ta kasar Sin yana ganin cewa, aikin mika iko ga kamfanoni da gwamnatin kasar Sin ta yi zai sa kaimi ga raya tattalin arzikin kasar. Wang Jun ya ce, "Babban canjin da aka samu a cikin shekara daya da ta gabata shi ne sakarwa kasuwa mara ta yadda za ta taka muhimmiyar rawa, yayin da ita ma gwamnati za ta taka nata rawarta yadda ya kamata, wannan zai sa kaimi ga kamfanoni kara yin takara a kasuwanni tare da raya tattalin arzikin kasar gaba daya."

Mutane da dama suna fakewa da maganar da ake cewa, "tattalin arzikin kasar Sin ya shiga sabon lokaci" wajen takaita canjin da aka samu a halin yanzu. A ganin masanan tattalin arziki, wannan sabon lokaci ya kunshi lokuta uku wato lokacin rage saurin samun karuwa, lokacin kyautata tsari da kuma lokacin daidaita manufofin sa kaimi ga raya tattalin arziki, sannan ana fuskantar matsaloli iri daban daban a sabon lokacin. Babban canjin da aka samu a lokacin shi ne saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya ragu daga fiye da kashi 10 cikin dari zuwa kashi 7.5 cikin dari. Babban masanin tattalin arziki na cibiyar sadarwa ta kasar Sin Fan Jianping ya yi tsammani cewa, ya kamata kowa ya bukaci tare da dace wa da wannan sabon lokaci. Ya ce, "Ya kamata a sake duba halin da tattalin arzikin kasar Sin yake ciki. Yanzu muna cikin lokacin canja saurin karuwar tattalin arzikinmu. Tabbas ne saurin karuwar tattalin arzikinmu zai ragu sannu a hankali a kokarin kyautata tsarinsa." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China