in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Abubuwan da ya kamata a sani kan cikakken zama karo na 4 na kwamitin tsakiya na JKS
2014-10-20 16:28:48 cri

A yau 20 ga wata da yamma, an bude cikakken zama karo na 4 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wanda kuma za a rufe a ran 23 ga wata a nan birnin Beijing. "Tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka" shi ne babban jigon wannan cikakken zaman taro. Kuma wannan ne karo na farko da aka sanya irin wannan jigon a wani cikakken zaman taro na jam'iyyar. Sabo da haka, ana son sanin kowane irin tasiri ne wannan cikakken zama zai kawo wa zaman rayuwar al'ummar kasar Sin baki daya. Tun daga yau, sashen Hausa na CRI zai fara gabatar muku da wasu jerin rahotanni game da wannan cikakken zama karo na 4 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Yanzu ga rahoton farko game da abubuwan da ya kamata a sani game da wannan cikakken zama.

"Ina fatan za a iya sa ido kan sana'o'in samar da abinci bisa doka. Sakamakon haka, masu yawon bude ido za su iya samun abinci mai inganci kamar yadda ya kamata a lardinmu na Shaanxi."

"Ina fatan za a iya fitar da dokoki da ka'idodi a yayin wannan cikakken zama, ta yadda masana'antu da jama'ar fararen hula za su iya samun adalci bisa doka."

A lokacin da wakilinmu yake intabiyu a kan titi, mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu kan yadda suke ganin za a iya tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka, ta yadda za a iya tabbatar da kawo wa jama'a adalci, alheri da mutunci.

A yayin wannan cikakken zaman taro, ba ma kawai za a tattauna muhimmin batun tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka da batun shirya ayyukan bunkasa tattalin arziki a karshen rabin shekarar da muke ciki ba, har ma lalle za a duba rahoton da kwamitin yaki da cin hanci da rashawa na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin zai gabatar, da canja guraban aikin yi na wasu muhimman jami'ai. Bugu da kari, za a kori wasu mambobin kwamitin tsakiya na jam'iyyar wadanda suka keta dokokin jam'iyya da na kasa, kuma yanzu ana gudanar da bincike kansu bisa doka daga cikin kwamitin tsakiya, har ma daga jam'iyyar a yayin wannan cikakken zama. Sabo da haka, ana ganin cewa, batutuwan yin gyare-gyare, da kafa sabbin dokoki da kuma kara azama wajen yaki da cin hanci da rashawa za su zama muhimman batutuwa a yayin wannan taron.

Me ya sa aka tabbatar da batun tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka da ya zama muhimmin jigo a wannan cikakken zama? Shehun malami Xie Chuntao wanda ke nazarin tarihin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a makarantar kwamitin tsakiya na JKS yana nuna cewa, "Sabo da babban sakatare Xi Jinping na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya fi mai da hankali kan yadda za a ba da jagoranci ga kokarin daidaita matsaloli. Ana taro ne domin kokarin daidaita matsaloli. Yanzu ana ganin cewa, akwai matsaloli iri daban daban da suke kasancewa kan yadda ake tafiyar da dokoki, da bin dokoki. Alal misali, wasu mutane ba su bi dokoki kamar yadda ya kamata ba. Har ma wasu hukumomin gwamnati sun yi amfani da ikonsu ba bisa doka ba. Bugu da kari, wasu kotuna ba su yi shari'a cikin adalci ba, har ma wasu alkalai suna karbar cin hanci da rashawa. Tabbas ne al'ummomin kasa su nuna rashin jin dadin kan irin wadannan al'amura. Sabili da haka, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya zabi batun tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka a matsayin muhimmin jigo a wannan cikakken zama."

Bayan da Xi Jinping ya zama babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a watan Nuwamba na shekarar 2012, ya taba bayyana tunaninsa sau da dama kan batun tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka. Alal misali, a yayin taron taya murnar cika shekaru 60 da kafa babban taron wakilan jama'ar kasar Sin, wato majalisar kafa dokokin kasar, ya sake jaddada muhimmancin tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka ga jama'ar fararen hula da ci gaban kasar gaba daya. Mr. Xi ya ce, "Dole ne mu karfafa aikin kafa dokoki a cikin muhimman fannoni, ta yadda za a iya tabbatar da samun bunkasuwa da yin gyare-gyare bisa doka. Dole ne mu bi dokoki a lokacin da muke tsai da kudurai kan batutuwan neman ci gaba da yin gyare-gyare. Bugu da kari, ya kamata mu kafa doka bisa ilmin kimiyya da kundin tsarin mulkin kasa ta hanyar dimokuradiyya, kuma ya kamata mu kyautata ajandar kafa doka domin cika buri da fatan jama'a da kuma samun goyon bayansu."

A ganin Mr. Zhu Lijia, direktan ofishin koyar da ilmin tafiyar da harkokin jama'a a makarantar koyon ilmin mulkin kasar Sin, "tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka" yana bayyana yadda kasar Sin ke kokarin kawar da matsaloli masu tsanani da suke kasancewa a kasar bisa doka. Mr. Zhu ya ce, "Wani muhimmin tunanin Xi Jinpin kan mulkin kasa shi ne tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka. 'Tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka' ba wata magana kawai ba ce, wata niyya ce da Xi Jinping ya sa bayan da ya dade yana nazarta abubuwan kasa bisa manyan tsare-tsaren bunkasa kasar. A cikin shekaru 5 ko 10 masu zuwa, idan za a iya cimma wannan buri na tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka, tabbas ne zaman al'ummarmu zai kara samun kyautatuwa, jama'a ma za su kara samun alheri, har ma za mu iya zamanintar da kasarmu kamar yadda muke fata." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China