Babban jami'in kwamitin tsaron MDD mai kula da harkokin siyasa Jeffrey Feltman, ya ce, tattaunawar da bangarorin Falasdinu da Isra'ila ke yi domin farfado da yanayin zaman lafiya, ya kai wani mataki dake bukatar taka tsan tsan.
Feltman wanda ya bayyana hakan ga wakilan kwamitin na tsaro, yayin da yake karin haske kan irin ci gaban da aka samu, don gane da batun farfado da yanayin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, ya kara da cewa, ya zama wajibi, bangarorin biyu su kaucewa daukar matakan gurgunta irin nasarar da aka cimma kawo wannan lokaci.
A cewar wannan jami'I, duk da irin kalubalen da tattaunawar ke fuskanta, ana iya cewa, an kai ga rage gibin dake tsakani sakamakon banbance banbancen ra'ayoyi. Ya ce, a baya bayan nan sanarwar ci gaba da kara ginin matsugunnan Yahudawa a yankunan yammacin kogin Jordan, da gabashin Jerusalem da Isra'ila ta ayyana, na cikin abubuwan da ka iya haifar da koma baya.
Tuni dai MDD ta bayyana matsayarta, ta kin amincewa da wannan mataki da Isra'ilan ta dauka, tare da bukatar dakatar da wadannan gine-gine. Feltman ya kara da bayyana kyakkyawar tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, a matsayin hanya daya tilo, da za ta kai ga biyan bukatun al'ummunsu, a fagen tabbatar da zaman lafiya da ingantaccen yanayin tsaro. (Saminu)