Mahukuntan al'ummar Falasdinu sun bayyana aniyar Isra'ila ta ci gaba da ginin matsugunnan Yahudawa, a matsayin wata barazana ga ci gaban tattaunawar da bangarorin biyu suke gudanarwa.
Wata sanarwa da babban jami'i mai shiga tsakani na al'ummar Falasdinu Saeb Erekat ya fitar, ta ce, sanarwar da Isra'ila ta fitar, don gane da gina karin gidajen Yahudawa har 20,000, a ranar Laraba na iya kawo tsaiko ga tattaunawar da ake ciki.
Erekat ya ce, tuni ma shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya umarci tawagar masu shiga tsakanin ta kasarsa, da ta tuntubi Amurka, da Rasha, da Sin, da ma kungiyar tarayyar Turai, domin neman agajinsu, wajen warware wannan batu.
Da ma dai tuni Amurka wadda ita ce ke jibintar shirya taron tattaunawar, ta bayyana matsayinta na kin goyon bayan ci gaba da ginin karin matsugunnan Yahudawan, tana mai kiran aikin gine-ginen da wani lamari da ya sabawa doka. (Saminu)