Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya ce, bangarorin siyasar Fatah da Hamas sun cimma nasarar dinke barakar da suka sha fama da ita tsawon shekaru 7 da suka gabata.
Cikin wani jawabi da ya yi ta kafar talabijin, jim kadan da rantsar da gwamnatin hadin kan Falasdinun, shugaba Abbas ya ce, hadin kan Falasdinawa muhimmin ginshiki ne, da zai share fagen cimma burika, da kudirorin al'ummarsa.
An dai gudanar da bikin rantsar da jagororin gwamnatin hadin kan Falasdinun ne a jiya Litinin, a birnin Ramallah dake yamma da gabar kogin Jordan.
Ministoci 13 ne suka ci laya yayin bikin rantsuwar, ko da yake wasu sabbin ministocin 4 ba su samu halartar bikin ba, sakamakon hana su shiga yankin na yammacin kogin Jordan da hukumomin Isra'ila suka yi. (Saminu)