in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fada ba bu cika wa kawai, ba zai taimakawa ci gaban tattalin arzikin Afirka ba, in ji jami'an kasa da kasa
2014-10-14 17:25:25 cri

Yanzu annobar Ebola na ci gaba da barazana ga rayukan al'ummar duniya, wadda kuma ta fi tsanani a yammacin Afirka. Amma duk da haka a wajen taron dandalin tattalin arzikin Afirka karo na 14 da aka shirya a cibiyar raya kasa ta kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki a kwanakin baya, wasu manyan jami'an kasa da kasa da suka hada da shugabar hukumar zartarwar kungiyar tarayyar kasashen Afirka Nkosazana Dlamini-Zuma, da mataimakin babban sakataren MDD Carlos Lopes, sun ce, idan aka kwatanta da cutar Ebola, yadda ake yin maganganu kawai ba tare da tabuka kome ba zai fi illa ga tattalin arzikin Afirka.

A shekarun baya, yayin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar koma baya, tattalin arzikin Afirka a nasa bangare na ta samun karuwa cikin sauri, lamarin da ya janyo hankalin al'ummar duniya sosai. Bisa alkaluman da kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta OECD ta bayar, an ce karuwar tattalin arzikin nahiyar Afirka a shekarar 2013 ta kai kashi 4 cikin 100, wanda ya zarce karuwar tattalin arzikin duniya gaba daya ta kashi 3 cikin 100, haka zalika, ana sa ran ganin samun karin saurin karuwar tattalin arzikin nahiyar Afirka a bana da kuma badi. Sai dai a ganin wasu manyan jami'an kasashe daban daban, har yanzu tattalin arzikin nahiyar bai samu zama da gindinsa sosai ba tukuna, kuma babu tabbacin cewa irin ci gaban da aka samu zai dore a nan gaba ba.

A cewar Nkosazana Dlamini-Zuma, shugabar hukumar zartarwar kungiyar tarayyar kasashen Afirka(AU), dalilin da ya sa ake samun tafiyar hawainiya a yunkurin sauya salon ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka, shi ne domin babu wata manufa mai inganci, kana hukumomin kasashen Afirka ba sa tabuka komai sai zancen fatar baki kawai. Hakan a cewar madam Zuma zai fi haifar da illa ga tattalin arzikin kasashen Afirka idan an kwatanta da annobar Ebola wadda a halin yanzu take janyo hankalin kasashen duniya sosai. Haka kuma, madam Zuma ta kara da cewa, sakamakon rashin tabuka abin azo a gani, darajar abin da kasashen Afirka ke samu a bangaren cinikayya yanzu kashi 2.2 cikin 100 ne kawai. Haka zalika, har yanzu kasashen Afirka na bukatar shigo da shinkafa da kayan lambu daga kasashen waje, duk da cewa suna da maka-makan filaye da muhalli mai kyau. Abun da ya kasance babban abin kunya da ake samu a karni na 21, in ji Madam Zuma.

A nasa bangare, mista Carlos Lopes, mataimakin babban sakataren MDD, ya ce, bazuwar annobar Ebola a wasu kasashen dake yammacin Afirka, da suka hada da Guinea, Laberiya, da Saliyo, za ta yi tasiri ga tattalin arzikin wadannan kasashen, amma hakan ba zai yi tasiri kan makomar tattalin arzikin nahiyar Afirka ba, idan aka yi la'akari da yadda tattalin arzikin kasashen 3 kan adadin tattalin arzikin nahiyar Afirka ba zai wuce kashi 1% ba. A ganin mista Carlos, makomar tattalin arzikin Afirka na dogaro kan sauyin da za a samu a tsarin tattalin arziki, da inganta aikin ilimi da harkokin gwamnati, gami da kyautata yanayin cinikayya a nahiyar Afirka baki daya.

A kokarin da ake na canza salon tattalin arzikin nahiyar Afirka, cibiyar raya kasa ta kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta kaddamar da wani shirin 'aikace-aikacen Afirka' a lokacin taron dandalin da aka kira. An ce, shirin na da nufin kafa wani dandali na musayar ra'ayi kan manufofin gwamnati tare da kungiyar kasashen Afirka AU, ta yadda kasashe daban daban dake Afirka za su yi mu'ammala sosai kan yadda za su shiga a dama da su a tsarin tattalin arzikin duniya, da kyautata tsarin su a fannin tattalin arziki. Wani muhimmanci ga wannan shirin shi ne an koyi darasi bisa manufofin da kasashen Afirka suka taba bullo da shi, ta yadda aka mai da kasashen da suka canza salon tattalin arzikinsu cikin sauri a matsayin abin koyi, wadanda suka hada da Kodibwa da Moroco.

Dangane da haka, babban sakataren kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki, mista Angen Gurria, ya ce ba a hana amfani da manufofi masu kyau a duniya ba, sabili da haka yana fatan ganin kasashen dake niyyar za su yi kwaskwarima tare da hada kai a tsakanin su, don musayar wasu fasahohin masu inganci.

Ban da haka kuma, yayin da jami'an suke tattaunawa kan sanyin da aka samu a salon ci gaban tattalin arzikin nahiyar Afirka, sun dajaranta hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, da gyare-gyaren da kasar Sin take yi a cikin gida wadanda ke da ma'ana sosai ga ci gaban nahiyar Afirka. A cewar tsohon firaministan kasar Italiya, mista Romano Prodi, hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta taimakawa kokarin raya tattalin arzikin nahiyar Afirka, gami da canza hanyar da sauran manyan kasashen suke bi wajen kula da huldar dake tsakaninsu da kasashen Afirka, lamarin da ya daga matsayin nahiyar Afirka a idanun duniya.

Dangane da wannan batu, minista mai kula da tsara manufofin gwamnati na kasar Togo, Kako Nubukpo, ya ce sakamakon hadin kan da ke tsakanin kasar Sin da Afirka, kasashen Afirka sun samu kayayyakin more rayuwar jama'a masu inganci, gami da fasahohi da kwararru. Ga misali, a shekarun baya, wasu daliban kasar Togo da yawa sun yi karutu a kasar Sin, wadanda suka koma kasar Togo tare da ilimi da fasahohi masu ci gaba,wadda daga bisani suka ba da gudunmowa ga ci gaban tattalin arzikin kasarsu. Har ila yau kuma, a cewar mista Nubukpo, yadda kasar Sin ke gudanar da gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, da kokarin kasar a fannin raya masana'antu, abubuwa masu kyau da kasar Togo da sauran kasashen dake nahiyar Afirka ya kamata su koya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China