in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karfafa dangantaka tsakanin Sin da Afrika domin daukan matakin shawo kan yaduwar makamai ba bisa ka'ida ba
2013-07-03 12:50:03 cri

Za'a iya cin gajiyar dangantaka tsakanin Sin da Afrika idan aka inganta shi na tsawon lokaci, ta yadda za'a iya aiwatar da shirye-shiryen magance yaduwar manya da kananan makamai ba bisa ka'ida ba a Afrika, in ji wassu masanan Sinawa.

A hirarsu da kamfanin dillancuin labarai na kasar Sin Xinhua, a lokacin da aka yi wani babban taro kan yadda za'a shawo kan yaduwar makamai ba bisa doka ba a nahiyar Afrika da aka yi a birnin Nairobi na kasar Kenya, masanan sun jaddada cewa, Sin na da babbar rawa da za ta taka wajen inganta sha'anin tsaro, zaman lafiya da daidaito a Afrika.

Zhang Chun, wani masani a kan dangantakar Sin da Afrika kuma malami a jami'ar hulda da kasashen waje dake Shanghai, ya yi bayanin cewa, kasancewar kasar Sin a wannan hadin gwiwwa zai taimaka ma nasarar dakatar da yaduwar makamai ba bisa ka'ida ba, wanda yake kawo sabon barazana ga nahiyar.

Mr. Zhang Chun ya lura cewa, tsare-tsaren harkokin waje na Sin na dauke da bukatar samar da zaman lafiya, tsaro da daidaito a nahiyar domin cimma burin cin gajiyar juna. Don haka, in ji shi, yaduwar makamai ba ma kawai yana tsananta fadace-fadace da kuma durkushe cigaba a nahiyar, har ma yana kawo illa ga ra'ayin da Sin ke da shi a nahiyar.

Malam Zhang Chun ya yi bayanin cewa, Beijing na daya daga cikin masu kokari na kasashen duniya na ganin sun magance yaduwar makamai ba bisa ka'ida ba a Afrika.

Kasar Sin ta taimaka ma shirye-shirye da dama da zai samar da zaman lafiya da tsaro a Afrika, da kuma magance yawaitar manya da kananan makamai. Tsaro, in ji shi, na daya daga cikin abubuwan da ke kawo cikas ga tattalin arzikin nahiyar.

Malamin kuma masani a harkar dangantaka tsakanin Sin da Afrika ya yi bayanin cewa, Sin ta dade tana taimakon hana tashin hankali da kuma samar da dabarun amfani da su bayan tashin hankalin domin sake gina nahiyar ta Afrika, don haka kalubalen kanana da manyan makamai yana kara tsananata yanayin da a kan shiga bayan fadace-fadace a kasashen da suka yi fama da hakan kamar su Libya, Somaliya, Sudan ta Kudu da kuma jamhuriyar demokradiya ta Kongo.

Malam Zhang Chun ya jaddada bukatar da ke akwai na shigar da gwamnatocin Afrika, shugabannin yankuna, kungiyoyi masu zaman kansu wajen tsara shirye-shiryen da za su kawo nasarar karbe makamai da aka same su ba bisa izini ba a wadannan kasashe, kuma a cewarsa, kasasncewar Sin a cikin wannan shirin zai kara jawo nahiyar Asiya gaba daya da ta shiga ayyukan cigaba a Afrika.

Dalilin yaduwa da kuma safaran makamai ba bisa ka'ida ba ya biyo bayan bullowar kungiyoyin 'yan ta'adda da kuma laifukan da ake aikata su tsakanin kasa da kasa a wurare da dama a nahiyar ta Afrika.

Ya kuma lura da cewa, sace mutane, musamman Sinawa, ana garkuwa da su a wuraren da ake hakar ma'adinai ya biyo bayan yawan makamai ne da ake ganin ta ko'ina ba bisa doka ba.

Shi ma a nashi tsokacin, wani malami a cibiyar ilimin harkokin da suka shafi hulda da kasashen waje Ouyang Liping ya jaddada cewa, ya kamata dangantaka tsakanin Sin da Afrika ta mai da hankali a kan yaduwar makamai ba bisa ka'ida ba.

A cewarsa, Sin ta fahimci muhimmancin samar da zaman lafiya, daidaiuwa da cigaba a Afrika. don haka za ta iya samar da taimako na wajen ayyukan yi domin a taimaki kasashen Afrika da su daidaita yaduwar makamai ba bisa ka'ida ba, saboda a hana isar su hannu miyagun kungiyoyi.

Kasancewar Sin a cikin shirye-shirye kamar su taimaka ma kara karfin ma'aikatan tsaro, samar da horo da ba da ilimi domin inganta kula da makamai zai taimaka wajen yaki da yaduwar makamai ba bisa ka'ida ba a nahiyar ta Afrika.

Malam Ouyang Liping ya kara da cewa, yawaitan musayar sojoji da kuma kafa cibiyoyi na gwaji tsakanin Sin da Afrika zai karfafa yakin da ake yi da yaduwar makamai ba bisa ka'ida ba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China