in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sarkakiyar manufofi da rashin isassun ababen more rayuwa ne ke dakile ci gaban Afirka
2013-05-02 14:04:10 cri

A ranar Laraba 1 ga watan Mayun nan ne aka bude wani babban taron kasashen duniya, na masu ruwa da tsaki kan harkokin ciniki da ci gaban tattalin arzikin nahiyar Afirka, a birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa. Taron wanda ya samu halartar wakilai da masana da dama, ya mai da hankali sosai ga nazarin dalilan da suka sanya nahiyar ta Afirka, gaza cimma cikakkiyar nasarar da take buri, duk kuwa da cewa, akwai alamun ci gaba da nahiyar ke samu a 'yan shekarun nan.

Da dama dai daga mahalarta taron na da ra'ayin cewa, nahiyar ta samu ci gaba a bara, da kason da ya haura matsakaiciyar nasarar da ragowar kasashen duniya suka samu, ko da yake dai, wannan nasara na gauraye da tarin matsaloli daga cikin gida. A watan Afrilun da ya gabata ne dai asusun ba da lamuni na IMF ya bayyana cewa, ma'aunin tattalin arzikin nahiyar Afirka na GDP, zai daga da kaso 5.6 bisa dari a shekarar nan ta 2013, wanda hakan ke nuna dagawar mizanin, sama da na ragowar kasashen duniya, wanda aka yi kiyasin ba zai wuce kaso 3.3 bisa dari ba. Asusun na IMF ya kuma ce, kasashen Swaziland, da Equatorial Guinea ne kadai ake hasashen za su samu koma bayan tattalin arziki a dukkanin fadin nahiyar ta Afirka a wannan shekara.

Yayin da ake tsaka da wannan taro, mataimakiyar babban darakta a kungiyar cinikayya ta duniya dake birnin Geneva Valentine Rugwabiza, ta gabatar da makala dake nuna cewa, duk da irin nasara da kasashe mambobin kungiyar cinikayya ta duniya daga nahiyar Afirka ke samu, sama da abin da aka tsammata, musamman cikin shekaru 3 da suka gabata, a lokaci guda ana iya cewa, gudanar da kasuwanci a nahiyar na da tsada matuka. Rugwabiza ta lasafta rashin isassun ababen more rayuwa, kamar rashin managartan hanyoyin sifiri, da rashin tallafawa mata, da tarin sarkakiyar manufofin hukuma, a matsayin manyan kalubalen da ya dace a shawo kansu.

Da yake nasa jawabi, ministan ciniki da masana'antun kasar Uganda Amelia Kyambadde, kira ya yi ga mahalarta taron, da dukkanin wakilan cibiyoyi da hukumomin da abin ya shafa, da su dauki wadannan kalubale tamkar wata dama ta habaka hada-hadar cinikayyarsu a nahiyar, yana mai ra'ayin cewa, da dama daga kasashen dake nahiyar Afirka, kofofinsu a bude suke ga 'yan kasuwa. Kyambadde ya ce, za a iya gane hakan idan aka kalli yadda nahiyar ke kunshe da kimanin kaso 12 bisa dari, na daukacin gurbataccen mai da iskar gas, da kuma kaso 40 bisa dari na ma'adinin gwal da ake hakowa a duk fadin duniya. Da yake amsa tambayar wakilin kamfanin dillancin labarun Xinhua, don gane da shin ko mallakar filayen noma da masu zuba jari ke yi wani tsari ne na kwace ga 'yan kasa kamar yadda wasu manazarta ke gani? Kyambadde ya ce, a ganinsa, hakan ba wani abin damuwa ba ne, muddin dai aka kiyaye sharuddan da hukumomin kasashen da ake hulda da su suka gindaya.

Wani rahoto da bankin zuba jarin na birnin Dubai mai suna "Alpen Capita" ya gabatar, don gane da masana'antun sarrafa abinci na kasashen dake yankin "Gulf", ya nuna yadda karancin kasar noma mai yalwa a zirin yankin Larabawa, da kuma yalwar irin wannan filaye a nahiyar Afirka masu karancin kudaden zuba jari, ka iya zama wata hanyar da za ta ba da damar yin hadin gwiwa, da bangarorin biyu za su ci gajiyarsa.

Bisa kididdiga dai, an ce, yankin "Gulf" mai arzikin man fetur, na sayo kimanin kaso 90 bisa dari na abincin da al'ummarsa ke bukata ne daga ketare. Hakan nema ya sanya babban darakta a cibiyar ciniki da masana'antun birnin Dubai, kuma daya daga jagororin shirya wannan taro Hamad Buamim, ya bayyana cewa, babu wata nahiya da za ta shige gaban nahiyar ta Afirka, a fagen ci gaba cikin shekaru masu zuwa. Buamim ya kara da cewa, birnin Dubai, zai ci gaba da kasancewa wata gada ta habakar harkokin cinikayya da zuba jari ga nahiyar ta Afirka, musamman ma tsakanin nahiyar da kasar Sin, dama ragowar nahiyar gabashin duniya baki daya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China