in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi kan yadda kwararrun Sin ke kallon sabuwar matsala ta yaki da ta'addanci a Afrika
2013-09-30 13:41:22 cri

"Mun kunyata da murkushe maharan cikin nasara." in ji shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a cikin wani jawabinsa ta talabijin, domin bayyana bajintar da sojojin kasar suka yi na dakile 'yan kungiyar Al-Shabaab na kasar Somaliya, bayan an kwashe fiye da kwana uku ana bata kashi tare da 'yan kungiyar Al-Shabaab da suka kai hari kan ginin kasuwanci na Westgate dake birnin Nairobi.

Bayan kura ta lafa, bincike kan wannan hari na Kenya ya tabbatar da cewa, mutane akalla 67 suka mutu yayin da 240 suka jikkata, duk da cewa bincike na cigaba domin gano ragowar mutanen da suka bata. Wannan hari shi ne mafi muni tun bayan harin kunar bakin wake na kungiyar Al-Qaida a cikin watan Agustan shekarar 1998 a kan ginin ofishin jakadancin Amurka wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 200, lamarin da ya cigaba da shafa bakin fanti ga tarmanuwar kasar Kenya a matsayinta ta "Lu'u lu'un gabashin Afrika" .

Baya ga wannan tashin hankali na kasar Kenya, abubuwan koma baya da dama sun faru kamar harin ginin hakar iskan gas na Aljeriya, sace-sace mutane da yin garkuwa da su a kasashen Nijar da Kamaru, matsalar arewacin kasar Mali, hare-haren kungiyar Boko Haram a Najeriya, wadannan misalai na nuna cewa, kwana tashi barazanar ta'addanci ta kai ga Afrika.

Kungiyoyin ta'addanci a Afrika na gudanar da ayyukansu, musamman ma a yammaci da arewa da kuma gabashin Afrika, in ji madam He Wenping, darektar cibiyar nazarin harkokin Afrika a jami'ar kula da zamantakewar jama'a ta kasar Sin.

Reshen kungiyar Al-Qaida a yankin Magreb wato AQMI, kungiyar Al-Shabaab ta Somaliya da Boko Haram sun kasance manyan kungiyoyi uku dake aiki a nahiyar Afrika, inda biyu na farko suke da alaka da kungiyar Al-Qaida, a cewar wannan masaniya.

Wadannan masu fashin baki sun bayyana cewa, akwai dalilai da suka sanya ayyukan ta'addanci yin kamari a wannan shiyya wato shi ne juyin juya hali da aka samu a wasu kasashen Larabawa, kasashen Tunisia, Masar, Libya da ma wasu kasashe sun shiga cikin mawuyacin hali da zaman dar dar, lamarin da ya kara karfafa karfin ta'addanci. Haka kuma matsalar mulki, da rashin tsare-tsaren tsaro masu inganci a cikin kasashen Afrika na kara tura wadannan kasashe cikin wani sabon nau'in barazana, ta'addanci ke nan na iyar mamaye nahiyar Afrika.

Matsalar rashin aikin yi ta zama wani jigo dake adabar matasa kuma wata dama ga kungiyoyin ta'addanci na samun magoya baya. Za'a iyar cewa, ta'addanci na kara tsanani a nahiyar Afrika. Ana iya cewa, akwai wuya da suka kai wa kasashen yammacin duniya hari a cikin kasashensu, masu kishin islama na kai hari kan 'yan kasashensu da kadarorinsu dake nahiyar Afrika.

A cewar madam He Wenping, ya kamata kasashen Afrika da farko su kyautata karfinsu na mulki, tare da karfafa cigaban tattalin arziki da na jama'a, abu na biyu shi ne kasashen Afrika su hada kansu wajen yaki da ta'addanci, domin yin hadin gwiwa na da babban karfi ne.

A halin yanzu a lokacin da ayyukan ta'addanci ke cigaba da bazuwa a duniya baki daya, gwamnatoci ya kamata su mai da hankali kan yin musanyar bayanai da kuma sa ido kan iyakoki. Haka kuma ya kamata gamayyar kasa da kasa ta kara samar da kayyayaki da taimako ga kasashen dake fama da ta'addanci.

A nasa bangare, mataimakin darektan sashen nazarin harkokin yammacin Asiya da Afirka a cibiyar nazarin huldar kasa da kasa ta kasar Sin, mista Xu Weizhong ya jaddada cewa, kasashen yammacin duniya, kamar yadda dokokin MDD suka ayyana su taimaka wa kasashen Afrika wajen yaki da ta'addanci ba tare da yin shisshigi ba cikin harkokinsu na cikin gida domin kaucewa wasu sabbin tashe-tashen hankali da matsaloli.  (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China