in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Amurka ya fara ziyararsa a nahiyar Afirka
2013-06-27 18:42:06 cri

Ranar 26 ga wata da safe, shugaba Barack Obama na kasar Amurka ya tashi zuwa nahiyar Afirka domin ziyararsa ta farko bayan da ya sake hawa kujerar mulkin kasar. Wani jami'in fadar shugaban kasar wato White House ya ce, a lokacin ziyararsa ta tsawon mako guda, zai mai da hankali kan habaka mu'amalar da ke tsakanin Amurka da kasashen Afirka ta fuskar kasuwanci da kuma inganta yin mu'amala da matasan Afirka.

Kasashe uku na Afirka da mista Obama zai kai ziyara a wannan karo sun fi wakilcin nahiyar ta Afirka, wadanda ke yammacin nahiyar, kudancin nahiyar da gabashin nahiyar. Zangon farko a ziyarar mista Obama ita ce kasar Senegal, wadda ba ta da yawan mutane, kuma ana samun kwanciyar hankali ta fuskar siyasa a kasar, kana tana daya daga kasashen Afirka da ke kulla dankon zumunci a tsakaninsu da Amurka. Kasar Afirka ta Kudu kuwa ta yi fice a nahiyar ta Afirka a fuskar bunkasuwar tattalin arziki da siyasa, lamarin da ya sa kasar ta kasance wani muhimmin zango a wannan ziyararsa. Ko da yake kasar Tanzaniya a baya take wajen raya tattalin arziki, amma a shekarun nan, ta samu saurin ci gaba a fannonin ayyukan hakar ma'adinai da yawon shakatawa, inda har aka mayar da ita tamkar wani abin misali wajen samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a nahiyar ta Afirka.

Dangane da ziyarar mista Obama a Afirka a wannan karo, wani jami'in gwamnatin Amurka da ke Afirka ta Kudu ya bayyana cewa, ziyarar shugaban za ta bude wa Amurka wata babbar kofa a Afirka ta fuskar kasuwanci.

A matsayinsa na shugaban farko bakar fata a tarihin Amurka, mista Obama ya samu amincewa daga kasashen Afirka a farkon lokacin da ya zama shugaban kasar. Sa'an nan a wurare daban daban shi kansa ya kan jaddada cewa, yana da jinin Afirka, amma duk da haka, bayan da ya hau kujerar mulkin kasar, a shekarar 2009 ya yi awoyi 20 ne kawai a wata ziyara a kasar Ghana. Ta haka, shugabanni da manazarta da dama na kasashen Afirka sun nuna bakin cikinsu kan manufofin da gwamnatin Amurka ke aiwatarwa kan Afirka karkashin shugabancinsa.

Ko da yake gwamnatin Obama ta sa fatan alheri sosai kan ziyarar Obama a kasashen Afirka a wannan karo, amma wasu batutuwan ba-zata sun dan rage armashin wannan ziyara, kamar ciwon da tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela yake fama da shi a halin yanzu. Sa'an nan kuma, a kwanan baya Edward Snowden, tsohon dan leken asiri na gwamnatin Amurka ya tono asirin gwamnatin na daukar dukkan matakan sa ido kan yanar gizo ta Internet. Ko da yake Obama ya jaddada mayar da Afirka tamkar muhimmiyar abokiya ta fuskar ciniki, akwai tabbacin cewa, za ta yi zaman daidai wa daida da kasashen Afirka? Yanzu ana shakkar cewa, ko Amurka za ta nuna amincewa wajen yin ciniki da Afirka cikin adalci ko a'a.

A yayin da kasashen Afirka na fama da babbar matsalar tsaro, kudin da Obama ya kashe wajen tabbatar da tsaron lafiyarsa a lokacin ziyara a wannan karo ya jawo suka matuka. An kiyasta cewa, za a kashe dalar Amurka miliyan dari daya wajen tabbatar da tsaron lafiyar Obama a wannan karo. Yayin da gwamnatin Amurka take aiwatar da manufar tsuke bakin aljihunta, Obama ya kashe makudan kudaden wajen ziyartar kasashen Afirka, inda lamarin ya jawo suka a kasar ta Amurka.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China