A jiya Litinin ne sabon shugaban tawagar yaki da cutar Ebola na MDD (UNMEER) Anthony Banbury ya sauka a kasar Ghana inda za a bude hedkwatar tawagar.
Kakakin MDD Stephane Dujarric shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan da isar sabon shugaban tawagar kasar ta Ghana, inda ya gana da tawagar farko da aka tura kasar ta Ghana don ganin an dauki matakan hana yaduwar cutar, ba da kulawa ga wadanda suka kamu da cutar tare da tabbatar da cewa, an samar da magungunan da suka kamata.
A makon da ya gabata ne babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya kafa sabuwar tawagar ta UNMEER wadda ita ce tawagar lafiya ta gaggauwa da MDD ta kafa da hada ayyukan majalisar na yaki na cutar Ebola wuri guda.
Ya zuwa yanzu dai cutar ta Ebola ta halaka mutane sama da 3000 a kasashen Liberia, Saliyo da kuma Guinea.
A yau Talata ne aka shirya Banbury zai yi wa manema labarai jawabi a Accra, babban birnin kasar Ghana. (Ibrahim)