Kungiyar raya kasashen kudancin Afrika SADC za ta tura masu sa ido a kan manyan zabuka a kasashen dake yankin ta wannan shekarar, kamar yadda gwamnatin Afrika ta Kudu ta bayyana a cikin wata sanarwa.
Mataimakin ministan kula da huldar kasa da kasa da hadin gwiwwa na kasar Afrika ta Kudu Luwellyn Landers wanda ya sanar wa manema labarai hakan a birnin Pretoria a ranar Alhamis din nan ya ce, kungiyar SADC za ta sa ido a kan babban zaben kasashen Mozambique, Botswana da Namibiya da za'a yi a cikin shekarar nan.
Kasar Afrika ta Kudu za ta dauki nauyin jigilar masu sa idon a kan zabukan a matsayinta na shugaban kwamitin tsare-tsare a kan siyasa, tsaro da ba da kariya na kungiyar.
A don haka, in ji shi, babban makasudin aikin shi ne don ba da kwarin gwiwwa ga daukaka ka'idojin kungiyar da tsarinta a kan zaben mulkin demokradiya, sannan za ta duba shirye-shiryen da aka aiwatar don cimma hakan dangane da manyan zabukan.
Da yake bayani a kan ayyukan masu sa idon a kan manyan zabukan, har ila yau ya ce, jami'an za su kuma gano kalubalolin da ka iya kawo cikas ga samun nasarar zaben a kasashen kungiyar. (Fatimah)