Shugaban kasar Botswana Ian Khama ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar SADC da za su gudanar da zabukansu a wannan shekara, da su gudanar da zabukan cikin gaskiya da adalci.
Shugaba Khama ya yi wannan kiran ne ranar Talata yayin da ya ke karbar sarki Letsie na III na Lesotho, inda ya ce, kasar za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace a zabukan da za a gudanar a yankin na SADC, ta yadda za su dace da dokokin zaben kungiyar.
Ya ce, a baya Botswana ta ce ba za ta shiga duk wani aikin sa-ido na zabe ba, tun bayan da aka yi watsi da kiran da ta yi na a sake kidaya kuri'an da aka kada a zabukan kasar Zimbabwe. Ko da ya ke kasar ta canza matsayinta ne, bayan da kungiyar ta SADC ta yi alkawarin daukar mataki kan wannan korafi.
A kwanan baya ne Khama ya janye kasar ta Botswana daga aikin kungiyar SADC na sa-ido kan harkokin zabe, saboda yadda ake ci gaba da watsi da korafin kasar game da tabka magudi a zabukan da aka gudanar a shekarar da ta gabata a kasar Zimbabwe. (Ibrahim)