in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
SADC ta jaddada aniyar tunkarar kalubalen da Lesotho ke fuskanta
2014-09-22 11:49:40 cri

Kungiyar raya kasashen kudancin Afrika SADC a jiya Lahadi 21 ga wata ta jaddada matukar bukatar da ke akwai ta tunkarar kalubalen da kasar Lesotho ke fuskanta a bangarorin siyasa da tsaro.

Wadannan kalubale sun hada da shirye-shiryen aiwatar da babban zabe cikin sauri, sake bude majalissar dokokin kasar, samar da daidaito a yanayin tsaro, sannan kuma da mai da da tsarin dokokin yadda ya kamata, in ji mai lura da harkokin ayyukan, kuma mataimakin shugaban kasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa.

Mr. Ramaphosa na magana ne kafin ziyararsa ta biyu da zai kai Maseru, babban birnin kasar ta Lesotho daga yau Litinin 22 zuwa kashegarin 23 domin aiwatar da amincewar yankin na maido da zaman lafiya, daidaito da samar da demokradiya a kasar.

Bayan nadin shi a wannan mukamin da shugabanin kasashe da gwamnatocin kungiyar da suka hada da jamhuriyar demokradiya na kongo da Tamzaniya, Mr. Ramaphosa ya kai ziyarar farko a Lesotho ranar Alhamis da ta gabata domin shiga tsakani game da warware rikicin siyasa da kasar wadda 'yar karamar tsibiri ne da kasar Afrika ta Kudu ta kewaye take fuskanta.

A lokacin ziyarar, Mr. Ramaphosa ya kai gaisuwan ban girma ga sarkin kasar Letsie na uku, ya kuma tattauna da shugabannin gamayyar kungiyoyin kasar karkashin jagorancin firaministan ta Thomas Thabane, da kuma manya da kanana jam'iyyun siyasa.

A ziyararsa ta biyu, ana sa ran Mr. Ramaphosa zai ci gaba da tattaunawa da duk jam'iyyun siyaya da sauran masu ruwa da tsaki a Lesotho domin taimakawa kasar ganin ta samu yanayi mai kyau ga al'ummarta, abin da zai ba su damar warware rikicin siyasar da suke fuskanta kamar yadda kundin tsarin mulki da dokokin kasar suka tanada, in ji wata sanarwar da kungiyar SADCn ta fitar.

Lesotho dai ta fada rikicin siyasa ne tun daga ranar 30 ga watan Agusta lokacin da wani yunkurin juyin mulki ya sa firaministan ta Thomas Thabane tserewa zuwa kasar Afrika ta Kudu. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China