in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya yaba da taron sulhun da ake guadanarwa a Somalia
2014-09-18 13:41:18 cri

Mukadashin wakilin magatakardan MDD a musamman a kasar Somalia Fatiha Serour, ya yi maraba da wani taro da aka fara a jiya Laraba a Kismayo, a inda ya ce, taron wani mataki ne da zai taimaka wajen karfafa samar da zaman lafiya a yankin tare da agazawa Somalia fafutukar da take yi na kara gina kasarta.

Mataimakin kakakin MDD, Farhan Haq, wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron 'yan jarida, ya ce, Serour ya yi kuma kira a kan 'yan kasar ta Somalia, da wadanda suka halarci taron da su samar da wani yanayi da zai haifar da shawarwari wadanda za su ba da gudumuwa wajen samun sulhu a duk fadin kasar ta Somalia.

Taron wanda shugaban kasar Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya bude, na da muradin bin sahun nasarorin da aka samu a yayin rattaba hannu a kan yarjejeniyar Addis Ababa ta watan Agusta na shekarar 2013, da kuma dorawa a kan nasarorin da aka samu bayan taron sasantawa da juna da aka yi a Mogadishu, a watan Nawumba na shekara ta 2013. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China