in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi tir da harin da aka kaiwa fadar gwamnatin Somaliya
2014-07-10 09:27:45 cri

Wakilin musamman na babban magatakardar MDD a kasar Somaliya Nicholas Kay, ya yi Allah wadai da harin da mayakan kungiyar Al-Shabaab suka kai fadar gwamnatin kasar Somaliya.

Masu aiko da rahotanni sun ce, kakakin MDD Stephene Dujarric ya tabbatar wa taron 'yan jarida aukuwar harin na daren Talata. Dujarric ya kuma hakaito kalaman Nicholas Kay, na cewa, wannan hari da Al-Shabaab ta kaddamar na cikin irinsa na baya-bayan nan da kungiyar ke kaiwa kan gine-ginen hukuma a kasar.

Kaza lika Mr. Kay wanda tuni ya gana da masu ruwa da tsaki game da tirkatirkar siyasar kasar ta Somaliya, ya ce, tabbatar da hadin kan sassan siyasar kasar ne kadai hanya daya tilo ta kawo karshen halin da ake ciki, sai dai ya bayyana takaicin ganin yadda masu burin wargaza kasar, ke iyakacin kokarin ganin hakan ya ci tura.

Daga nan sai Kay ya nanata kudurin MDD na goyawa al'umma, da mahukuntan kasar ta Somaliya baya, a kokarinsu na dawo da yanayin zaman lafiya da lumana a dukkanin fadin kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China