in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na kokarin samar da taimakon agaji ga Somalia
2014-07-09 10:50:03 cri

Babban jami'in samar da taimakon agaji na MDD a Somalia ya yi kira a kan kasashen duniya da su samar da agaji na gaggawa, domin taimakawa hukumomin bayar da taimakon agaji, wadanda ke samar da taimakon abinci na gagggawa ga 'yan kasar Somalia.

Babban mai gudanar da ayyukan agaji na MDD a kasar Somalia Philippe Lazzarini, ya yi gargadi a cikin wata sanarwa da aka bayar a Nairobi, cewa, kasar ta Somalia na cikin barazanar kara komawa cikin matsalar bukatar taimakon agaji, musamman saboda karancin abinci da karuwar cututtuka da hali na rashin tsaro.

Kamar yadda jami'in na MDD ya bayyana, duk da kasancewar matsalar karancin taimako na agaji na ci gaba da tabarbarewa a Somalia, kudaden da ake nemawa kasar ta Somalia sun yi karanci da kasa da kashi 25 bisa dari.

Lazzarini ya ci gaba da cewar, akwai gibin kusan dalar Amurka miliyan 700, wadanda har yanzu ake bukata domin samar da taimakon agaji nan da zuwa karshen shekara ta 2014 ga mutane miliyan 2.9, wadanda ke fafutukar samun abin da za su ci.

Kididdiga ta baya-bayan nan daga hukumar samar da abinci da ayyukan gona ta MDD FAO ta yi gargadi cewar, matsalar karancin abinci a Somalia za ta kuma tabarbarewa, a watanni masu zuwa, sannan kuma tuni aka lura da cewar, akwai matsalar fari a wasu sassa na kasar saboda karancin ruwan sama. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China