in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CERF ya ba da taimako domin rigakafin kyanda a Somalia
2014-07-15 10:19:03 cri

Asusun ba da agajin gaggawa na MDD ko CERF a takaice, ya fidda kudi da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 1 da dubu dari 4, domin gudanar da aikin yaki da barkewar cutar kyanda a kasar Somalia.

Hakan dai a cewar mukaddashin kakakin MDD Farhan Haq, ya biyo bayan barkewar cutar ta kyanda a Somaliyan, lamarin da yanzu haka ke barazana ga rayukan dubban yara kanana a kasa.

Haq ya kara da cewa, tuni ofishin lura da ayyukan jin kai na MDD OCHA, ya tsara kashe wadannan kudade a fannin yiwa yara 'yan kasa da shekaru biyar su kimanin rabin miliyan rigakafin wannan cuta, musamman a yankunan da cutar ta fi kamari, ciki hadda Banadir, da Lower Juba da kuma Puntland.

A cewar ofishin asusun yara na UNICEF, daga watan Maris zuwa Afirilun bana, adadin wadanda ake zaton sun kamu da cutar ya kai 1,350, adadin da ya dinka na makamancin wannan lokaci a bara har rubi 4. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China