in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta karfafa karfin sojojinta domin kare kanta, in ji shugaba Vladimir Putin
2014-08-30 16:53:12 cri
Kasar Rasha ta karfafa karfinta na nukiliya da kuma samarwa sojojinta makamai masu inganci kirar baya bayan nan domin kare kanta, in ji shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a ranar Jumma'a.

"Ya kamata mu san muna kariyar kanmu da kuma samun damar aiwatar da shirye-shiryenmu na tattalin arziki da na jama'a", in ji Putin a yayin wani dandalin matasa a yankin Tver dake cibiyar kasar Rasha, a wani labarin da kamfanin dallancin labarai na Interfax ya rawaito.

Hukumomin Moscou ba za su shiga cikin wasu yake-yaken soja na gama gari ba, amma kuma a shirye suke cikin shirin ko ta kwana domin dakatar da duk wani hari kan kasar Rasha, in ji shugaba Putin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China