A kwanan baya, jaridar new Zurich ta Switzerland ta bada labarai guda biyu masu taken "Marayun kabilar Tibet ba ainihin marayu ba ne" da "Rokon gafarar Dalai Lama na da muhimmanci", inda aka fallasa yadda kungiyar Dalai Lama ta yi karya ta dauki wasu yaran kabilar Tibet a matsayin marayu domin tura su zuwa Switzerland a dan dole.
Yayin da take amsa tambayar wani dan jarida dangane da wannan batu, madam Hua ta yi bayanin cewa, kasar ta lura da wannan labari. A sakamakon makasudin siyasa na Dalai Lama na 14 na kawo baraka ga jihar Tibet daga kasar Sin, da gangan ne ya shirya wannan karya, wadda ta yi sanadiyyar rabuwar yara daga iyalansu sama da dari daya. Danyen aikin kungiyar Dalai Lama ya taka hakkin yara sosai, tare da saba da halayen bil'adam. Kamata ya yi duk wanda yake da tausayi da kuma