A cewar wani rahoto mai suna Generation 2030/Africa, alkaluma mafi girma na haifuwa da yawan matan da suka kai shekarun haifuwa suna da sakamakon dake nuna cewa, a tsawon shekaru talatin masu zuwa, a dunkule za'a aifuwar haifi jarirai biliyan biyu a Afrika, yawan al'ummar Afrika zai karu da kashi biyu, kana yawan kananan yara masu kasa da shekaru 18 da haifuwa zai karu da kashi 2/3 domin kai ga cimma yara kusan biliyan daya.
Ta hanyar zuba jari a halin yanzu ga yara, a fannin kiwon lafiya, ilimi da kariya, Afrika zata iyar samun babban alfanun tattalin arziki kamar yadda wasu yankuna da wasu kasashe suka samu bisa karuwar yawan al'umma daidai da wannan in ji rahoto. Duk da cewa adadin wajen ganin yara sun rayu bai samu kyautatuwa ba a Afrika, nahiyar na cigaba da samun rabin yawan mace macen kananan yara a duniya kuma wannan kaso zai iyar haurawa zuwa akalla kashi 70 cikin 100 a shekarar 2050.
Haka kuma rahoton ya bayyana yaran Afrika 3 cikin 10 na rayuwa cikin yankuna masu hadari da yake yake-yake suka shafa, kana kashi 60 cikin 100 na mutanen Afrika zasu iyar zaman rayuwa a cikin birane nan da shekarar 2050.
Haka kuma rahoton ya bukaci da a maida hankali musammun ma kan Najeriya da tuni take da adadin haifuwa mafi girma a nahiyar da zai iyar zama kwata kwata haifuwa daya bisa goma a duniya nan da shekarar 2050. (Maman Ada)