in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar MDD ta yi shawarwari da bangarori daban daban na Libya kan kawo karshen rikici
2014-08-09 16:52:10 cri
Kamfanin dillancin labaru na Libya ya ba da labarin a ranar 8 ga wata cewa, yanzu mataimakin wakilin musamman na babban sakataren MDD kan batun Libya al-Ahmad yana yin shawarwari da bangarori daban daban na Libya domin kawo karshen rikicin a birnin Tripoli, hedkwatar kasar.

Mafi yawan membobin tawagar dake karkashin jagorancin al-Ahmad sun zo daga tawagar musamman ta nuna goyon baya da taimakawa Libya ta MDD. Wannan tawaga za ta yi bincike kan bukatar jin kai a kasar, da neman hanyar sassauta wahalhalun jama'a dake fama da rikici.

Kamfanin dillancin labaru na Libya ya rawaito kalaman al-Ahmad cewa, tawagarsa za ta kokarta kawo karshen rikicin cikin dogon lokaci a kasar tare da taimakon kasashen duniya baki daya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China