in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da samun rikice-rikice a kasar Libya
2014-07-28 14:50:25 cri
Tun daga ranar asabar 26 zuwa lahadi 27 ga wata, an yi ta rikici a birnin Benghazi dake kasar Libya, wanda ya haddasa mutuwar mutane a kalla 36.

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Reuters ya bayar, an ce, sojojin musamman na kasar Libya da dakarun Islam na kasar sun yi dauki ba dadi a daren ranar asabar a birnin Benghazi, rikicin ya dauki lokaci har kashegari safiyar ranar lahadi 27 ga wata. Kafar yada labarai na BBC ya ba da labari cewa, rikicin ya faru ne sakamakon harin da dakarun suka kai ga sojojin dake Benghazi, hakan kuwa ya haddasa mutuwar mutane a kalla 36.

Kamfanin Reuters ya ruwaito kididdigar da gwamnatin kasar Libya ta bayar cewa, yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sakamakon rikice-rikicen da aka samu a biranen Tripoli da Benghazi a cikin makwanni biyu ya kai 150, wadanda yawancinsu fararen hula ne.

Halin ba-dadi da ake ciki a kasar Libya shi ma ya kawo barazana ga tsaron 'yan kasashen waje dake kasar Libya. Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar Masar ya bayar, an ce, yayin da ake yin musayar wuta a tsakanin kungiyoyin dakaru daban daban na kasar Libya, wata roka da aka harba ta fada wata unguwa mai tarin jama'a 'yan kasar Masar a ranar asabar din, wanda ya haddasa mutuwar mutane 23. Ban da wannan kuma, ofishin jakadancin kasar Birtaniya da ke kasar ya bada labari cewa, an kai hari ga ayarin ofishin jakadancin a kan hanyarsu daga Libya zuwa Tunisia a ranar lahadi 27 ga wata, sai dai babu wanda ya mutu ko raunata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China