Yawan jarin da Sin za ta zuba ga kasashen waje a shekaru 5 masu zuwa zai karu da dala biliyan 500
A ranar 2 ga wata a birnin Bangkok dake kasar Thailand, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya halarci bikin bude taron koli na tattaunawa a tsakanin Sin da kungiyar kawancen kasashen kudu maso gabashin nahiyar Asiya (ASEAN), inda ya bayyana cewa, yawan jarin da Sin za ta zuba ga kasashen waje a shekaru 5 masu zuwa zai karu da dala biliyan 500, ya ce Sin za ta shigar da kayayyakin da darajarsu ta wuce dalar Amurka biliyan 10000 daga kasashen waje, kana yawan Sinawa da za su je kasashen waje don yin yawon shakatawa zai wuce miliyan 400.
Wang Yi ya nuna cewa, a halin yanzu, Sin da kungiyar ASEAN suna shiga sabon lokacin raya dangantakarsu. Don haka kamata ya yi bangarorin biyu su zurfafa hadin gwiwa, yin kokarin inganta yankin yin ciniki cikin 'yanci nasu wato CAFTA, kara yin mu'amala da juna, hada kai kan teku, kyautata tsarin hadin gwiwa a yankin, sada zumunci a tsakanin jama'arsu, yin hadin gwiwa a fannin kiyaye tsaro, da warware matsalolinsu ta hanyar yin shawarwari cikin adalci. (Zainab)