Rahoton ya nuna cewa, duk da halin rashin samun ci gaban tattalin arzikin duniya da karuwar rikice-rikice da ke faruwa a nahiyar Afirka, tattalin arzikin Afirka a shekarar 2013 ya karu da kashi 4 cikin dari, wanda ya ninka sau biyu bisa na dukkan duniya. Kasashe masu samun karancin kudin shiga sun fi samun bunkasuwar tattalin arziki a Afirka, amma manyan kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa a Afirka ba su samu saurin bunkasuwar tattalin arziki ba. Kuma tattalin arzikin kasashe masu samar da man fetur ya ragu a sakamakon raguwar yawan man fetur da suke hakowa, wanda ya yi kasa da kwatankwacin yawan saurin bunkasuwar tattalin arziki na Afirka. (Zainab)