Shugaban ya bayyana hakan ne a wani umarni da ya bayar a daren ranar Lahadi, inda ya umarci hukumomin da abin ya shafa, da su ba da fifiko ga aikin ceton rayukan jama'a, rage jikkatar mutane tare da bayar da tabbaci wajen tsugunar da wadanda bala'in ya shafa.
Ya kuma yi kiran da a hada karfi da karfe wajen aikin bayar da agaji tare da kara daukar matakai don hana aukuwar bala'o'i bayan faruwar girgizar kasar.
A ranar Lahadi ne girgizar kasar mai karfi maki 6.5 mai zurfin kilomita 12 ta abkawa a garin Longtoushan, kilomita 23 kudu maso yammacin gundumar Ludian ta lardin Yun'nan, lamarin da ya halaka mutane 175 tare da jikkata mutane 1,400 kana wasu 181 suka bace. (Ibrahim)