in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD da Amurka sun yi shelar tsagaita wuta a Gaza
2014-08-01 10:51:47 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon da sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry sun bayyana cewar, dokar tsagaita wuta ta awowi 72, a rikicin da ake yi a zirin Gaza, za ta kama aiki a ranar Juma'a, ranar 1 ga watan Agusta, a daidai karfe 8 na safe agogon kasar.

Kakakin babban sakataren MDD, Stephane Dujarric ya ce, wata sanarwar hadin gwiwa, wacce Ban da Kerry suka gabatar ta nuna cewar, tsagaita wuta za ta yi kwanaki ukku ne kacal sai fa idan an amince da kara tsawonta, kuma a lokacin tsagaita wuta sojojin dake kasa ba za su gusa daga inda suke ba.

Sanarwar ta gabatar da roko ga dukannin bangarorin biyu, da su nuna hallaya ta hakuri, har ya zuwa lokacin da tsagaita wutar za ta fara aiki, kuma an bukaci bangarorin biyu da su cika alkawurran da suka amince za su girmama a yayin tsagaita wutar.

Sanarwar ta ce, tsagaita wutar na da mahimmanci domin za ta ba da dama ga farar hula damar ta samun taimakon agaji, da kuma daman a gudanar da muhimman ayyuka da suka hada da binne gawawwakin wadanda suka mutu, da kuma kulawa da wadanda suka sami raunuka tare da kara tanadin abinci.

Hakazalika ita ma kungiyar kishin Islama ta Hamas da sauran bangarori na Palasdinu sun amince da tsagaita wutar na awowi 72 a yakin da suke yi da Isra'ila.

Wani babban jami'i na Hamas Izzat al-Resheq, wanda ke zaune a Qatar, kuma na hannun daman shugaban Hamas Khaled Meshaal, ya tabbatar da tsagaita wutar a shafin shi na Internet.

Ita ma Isra'ila ta bayar da tabbacin amincewa da tsagaita wutar na awowi 72 a yakin da take yi da Hamas, kamar dai yadda wani babban jami'in Isra'ila ya bayyana. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China