in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta yi allawadai da hare-haren Isra'ila kan Gaza
2014-07-23 10:02:33 cri

Gwamnatin kasar Nijar ta yi allawadai da hare hare ta jiragen saman da sojojin Isra'ila suke kai wa kan zirin Gaza.

A cikin wata sanarwar da aka fitar a ranar Talata, gwamnatin Nijar, duk da imanin cewa, Isra'ila tana da 'yancin kare iyakokinta, gwamnatin Nijar ta bukaci Isra'ila da ta kawo karshen manufarta ta mamaye da na mulkin mallaka da kangiyar ta yi wa Gaza, wadanda suka kasance muhimman dalilan boren na neman 'yancin al'ummar Falasdinawa.

Haka kuma gwamnatin Nijar ta yi kira da babbar murya ga sakatare janar na MDD da mambobin kwamitin tsaro na MDD da su bullo da wata munafur diplomasiyya ta gari da za ta taimaka ga kawo karshen munanan laifuffukan keta hakkin dan adam a Gaza, da kuma aza tubulin cimma wata mafita cikin adalci da karko game da rikicin Isra'ila da Falasdinu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China