in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza
2014-07-28 15:55:13 cri

Kwamitin tsaro na MDD ya bukaci kasar Isra'ila da kungiyar fafutuka ta Hamas da su rattaba hannu a kan yarjejeniyar tsagaita wuta, domin a kawo karshen asarar rayukan jama'a da ake ci gaba da yi a fadan da ake fafatawa a zirin Gaza, a cikin 'yan makonnin da suka shige, fadan ya haddasa asarar rayuka Palasdinawa 1030 da kuma sojojin Isra'ila 43.

Kwamitin tsaron na MDD ya gabatar da kiran tsagaita wuta a cikin wata sanarwa mai girma, wadda kasashe 15 dake karkashin MDD suka amince da ita, a wani taro karo na biyu da aka yi a cikin tsaken daren Litinin.

Kwamitin tsaron ya bukaci bangarorin Isra'ila da na Palasdinu da su amince tare da wanzar da tsagaita wuta, tun daga lokacin karamar salla, da kuma bayan sallar, domin taimakon jama'ar da rikicin ya rutsa da su.

Kwamitin tsaron ya kuma bukaci dukanin bangarorin biyu, da su ci gaba da gudanar da tattaunawa domin samar da tsagaita wuta mai dorewa, wacce dukanin bangarorin biyu dake yankin na zirin Gaza za su girmama. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China