in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta tura runkunin sojoji na biyu a Mali
2014-08-01 10:41:19 cri

Rukunin sojojin Nijar na biyu, dake kunshe da motoci kusan ishirin, dauke da daruruwan sojojin Nijar sun bar birnin Niamey a ranar Alhamis domin isa makwabciyar kasar Mali, bisa tsarin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Mali MINUSMA, in ji wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Rukunin na biyu na kunshe da manyan jami'an tsaro da sojoji, da m'aikatan kwana kwana, za su tsaya a kasar Mali har tsawon shekara daya.

Wadannan jami'an tsaro sun samu horo na kwanaki 45 a garin Ouallam mai nisan kilomita 100 daga arewacin birnin Niamey, kan ayyukan wanzar da zaman lafiya kamar yadda dokokin MDD suka tanada.

Sojojin dake cikin wannan sabon rukuni, za'a jibge su a biranen Gao, Ansongo da Menaka domin maye gurbin sojojin Nijar dake aikin wadannan yankuna tun a cikin watan Agustan shekarar 2013. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China