in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi allah wadai da kisan sojin kiyaye zaman lafiya a Mali
2014-07-01 10:39:55 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi suka da kakkausar murya a game da kashe wani soja na kiyaye zaman lafiya a kasar Mali, tare da jaddada cewar, wannan kisan kan da aka yi, ba zai sa MDD ta ja baya ba, a game goyon bayan da take baiwa jama'ar Mali, a fafutukar da suke yi, na kawo zaman lafiya mai dorewa a kasarsu.

Kakakin babban sakataren MDD ya fada a cikin wata sanarwa cewa, Ban Ki-moon ya yi allah wadai da harin da aka kai kilomita talatin a yammacin Timbuktu, inda wani bam da aka dana, ya kasha wani soja, 'dan asalin kasar Burkina Faso, mai gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya, tare da raunata wadansu sojojin kiyaye zaman lafiya guda 6. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China