in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi suka kan kisan sojin kiyaye zaman lafiya a Mali
2014-07-02 12:00:23 cri

Kwamitin tsaro na MDD ya yi suka da kakkausar murya a game da kashe wani sojin kiyaye zaman lafiya a kasar Mali, tare da kira a kan gwamnatin Mali, da ta gaggauta bincike a kan harin da aka kaddamar, tare da tilasatawa wadanda ke da hannu fuskantar shari'a.

Dukanin mambobin 15, dake cikin kwamitin tsaro na MDD sun yi allah wadai da kakausan kalamai, a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, a game da bam din da aka dana, kilomita 30 daga yammacin Timbuktu a Mali, a ranar Litinin, wanda ya yi sanadiyyar hallaka wani soja, 'dan kasar Burkina Faso, dake aiki da sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD., tare da raunata wasu sojoji 6 masu gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a Mali. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China