Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon a Jiya Litinin 17 ga wata ya amince da nada Manjo Janar Jean Bosco Kazura, 'dan kasar Rwanda a matsayin babban kwamandan rundunar kiyaye zaman lafiya na majalissar a kasar Mali wato MINUSMA.
Janar Kazura zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan gobe na Yuli, kamar yadda tsarin kwamitin tsaro na majalissar mai lambar 2100 na zaman da aka yi ranar 25 ga watan Afrilun bana ya tanada, in ji mataimakin kakakin majalissar Eduardo Del Buey a bayaninsa ma manema labarai.
A watan Afrilun wannan shekarar, kwamitin tsaro na MDD ya amince da karin sojoji 12,600 na rundunar kiyaye zaman lafiya da za su isa kasar Mali a ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa, kuma za su yi aiki na tsawon watanni 12.
Babban aikin rundunar shi ne taimaka ma samar da yanayin siyasa mai nagarta a kasar ta Mali, kamar yadda kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU, da kuma kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS suka shirya.
Sabon kwamandan Jean Bosco Kazura, 'dan kasar Rwanda yana da kwarewar aiki a gida da kasashen waje, tare da jagorancin rundunar da ma'aikata har na tsawon fiye da shekaru 24. (Fatimah)