in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya tsawaita wa'adin aikin tawagar MINUSMA
2014-06-26 10:09:55 cri

A zaman da ya gudanar na ranar Laraba, kwamitin tsaron MDD ya amince da tsawaita wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta kasar Mali MINUSMA da shekara guda.

Sabon wa'adin da mambobin kwamitin tsaron suka amince da shi dai zai kare ne a ranar 30 ga watan Yunin shekara mai zuwa. Kuma karin wa'adin ya biyo bayan halin rashin tabbas ta fuskar tsaro, da kuma ci gaban ayyukan ta'addanci dake ciwa, arewacin Mali, da ma sauran yankunan Sahel tuwo a kwarya.

Kwamitin tsaron dai ya jaddada manufofin wannan tawaga, da suka hada da wanzar da zaman lafiya da kare rayukan fararen hula, tare kuma da tallafawa aikin sulhu da yafiya tsakanin sassan al'ummar kasar Mali.

Kaza lika ana fatan tawagar ta MINUSMA za ta ci gaba da kokari, wajen marawa mahukuntan kasar baya a fagen kaiwa ga cimma daidaito, bisa halin da ake ciki yanzu haka a kasar.

To sai dai duk da dan ci gaba da aka samu a bara, ayyukan wannan tawaga sun hadu da koma baya, duba da yadda al'amura suka kara tabarbarewa a Mali tun daga farkon shekarar nan ta 2014, matakin da ya sanya kwamitin tsaron MDDr sake duba yiwuwar kara wa'adin aikin tawagar ta MINUSMA. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China