A gun taron manema labarun da aka yi a wannan rana, Tayeb Belaiz ya nuna cewa, bisa sakamakon da aka bayar, Abdelaziz Bouteflika ya sami kuri'u na kashi 81.5 cikin dari, yayin da babban abokin hamayyarsa, tsohon firaministan kasar Ali Benflis ya sami kuri'u na kaso 12.18 bisa dari, yawan kuri'un da sauran 'yan takara suka samu bai wuce kaso 4 cikin dari ba. Bisa kundin tsarin mulkin kasar Algeira, wanda ya sami kuri'u da ya wuce kaso 50 bisa dari ya ci zaben kai tsaye.
Tayeb Belaiz ya bayyana cewa, yawan masu kada kuri'u da aka yi rajista ya kai fiye da miliyan 22.871, yayin da yawan mutane da suka kada kuri'u ya kai na kashi 51.7 bisa dari daga cikinsu. Ya kuma jaddada cewa, sakamakon da aka gabatar na wucin gadi ne, kana kwamitin tsarin mulkin kasar zai gabatar da sakamako na karshe.
Abdelaziz Bouteflika mai shekaru 77 a duniya zai cika wa'adinsa har zuwa shekarar 2019. (Amina)