Mohammed Sobeih ya bayyana hakan ne a jiya Asabar 15 ga wata, bayan kammala shawarwari da ministan harkokin wajen Algeria Ramtane Lamamra. Inda ya ce kamata ya yi babban zaben dake tafe, ya haifar da sakamako mai kyau.
Tawagar sa ido ta kungiyar AL, dake karkashin jagorancin mista Sobeih ta isa Algeria a ranar 12 ga wata, inda ta yi shawarwari da hukumomin gwamnatin kasar, da sauran masu ruwa da tsaki.
Za dai a gudanar da babban zaben kasar ta Algeria ne a ranar 17 ga watan Afrilu mai zuwa, inda 'yan takara 6 za su shiga zaben, ciki har da shugaban kasar Abdelaziz Boutefilika.
An labarta cewa, cikin kungiyoyin da zasu tura jami'an sa ido don ganin yadda zaben zai gudana, hadda MDD, da kungiyar AL, da kungiyar tarayyar kasashen Afirka. Sauran sun hada da kungiyar tarayyar kasashen Turai, da kungiyar hadin gwiwar kasashen Musulmi da sauransu. (Fatima)