Kamfanin jiragen sama na Arik wanda shi ne ke kan gaba a cikin kamfanonin jiragen saman kasuwanci na Najeriya tare da hukumar kula da jiragen sama ta kasa da kasa IATA sun saka hannu a kan wata yarjejeniyar bude shafi a yanar gizo domin inganta ayyuka.
Wannan yarjejeniyar dai za ta ba da kafa ga amintattun dillalai na hada-hadar sufurin jiragen sama su biya kudin tikitin jirgi ta asusun ajiyarsu, in ji kamfanin jiragen sama a ranar Laraban nan.
A cikin sanarwar da ya fitar, kamfanin ya yi bayanin cewa, wannan kafar ta yanar gizo ya maye gurbin tsarin da ake amfani da shi wato GDS, domin wannan, yana baiwa dillalan sufurin jiragen sama damar duba nawa ne kudin tikitin jirgin ba tare da sun bi wata hanya ba, kuma wannan kafar za ta ba da cikakken bayani game da cinikin da dillalai suka yi wa kamfanin. (Fatimah)