Ana sa ran dai ziyarar ta Mr. Ban zuwa wasu yankunan gabas ta tsakiya wadda zai fara a Lahadin nan, za ta zama tamkar karfafar gwiwa ga sassan biyu, wajen kokarin kawo karshen tashe-tsashen hankula, da kuma share fagen hadin kai tsakanin su da sauran masu ruwa da tsaki daga shiyyar, da ma na sauran kasahen duniya dake da niyar kawo karshen halin da ake ciki yanzu haka.
Wata sanarwa da kakakin babban magatakardar MDDr ya fitar a ranar Alhamis ta hakaito Mr. Ban na kira ga sassan biyu da su dakatar da kaiwa juna hare-hare, tare da tabbatar da kare rayukan fararen hula, da jami'an MDDr, kana su tabbatar da damar shigar da kayayyakin jin kai ga sassan da ake bukatar su.
Mr. Ban dai zai fara ziyarar ta sa ta wannan karo ne da birnin Doha na kasar Qatar, sai kuma kasar Kuwait, kafin ya ziyarci birnin Alkahira na Masar, da biranen Jerusalam da Ramalla, ya kuma karkare da birnin Amman na kasar Jordan.(Saminu Alhassan)