Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wang Min, ya ce, ya kamata a samar da wata mafita mai dorewa da daidaito a siyasance, wacce za ta magance tashin hankalin da kasar Ukraine ta shiga.
Wang Min ya gabatar da wadannan shawarwari ne a yayin da yake jawabi a kan halin da kasar Ukraine ke ciki, ga wani taron kwamitin tsaro na MDD a ranar Talata.
Wang Min ya kara da cewar, kasar Sin na cikin damuwa saboda a wasu sassa na Ukraine, ana ci gaba da fama da matsalar tashin hankali da fada da makamai da kuma rikice-rikice, a kai a kai, hakan zai haifar da masifa a kan jama'a da dukiyoyinsu.
Bisa la'akari da kalaman tsagaita wuta, da kuma shirin zaman lafiya daga shugaban kasar Ukraine, Petro Poroshenko, Wang ya kara jaddada cewar, za'a iya magance matsalar Ukraine ne kawai ta hanyar siyasa, ya kuma kara da cewar, kasar Sin, a shirye take ta rungumi duk wani kokari da za'a yi, na kwantar da wutar rikicin Ukraine.
Mr. Wang Min ya yi fatan cewar, dukanin kungiyoyin za su natsu tare da nuna sanin ya kamata, da kuma yin amfani da wannan dama da aka samu ta tsagaita wuta, wajen amincewa da juna, tare da wanzar da sharuddan tsagaita wuta a wuraren da ake tashin hankali domin a samar da yanayi na gari, da zai zaburar da magance matsalar kasar a siyasance. (Suwaiba)