in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ukraine ta kwato wasu karin birane guda 4 dake gabashin kasar
2014-07-07 10:44:39 cri

Dakarun Ukraine sun kafa tutar kasarsu, a wasu karin birane hudu dake gabashin kasar, sai dai har yanzu ba su samu nasarar kame inda 'yan tsagera suka yi kaka gida ba.

Ministan tsaro na Ukraine Valeriy Heletey, da kuma babban hafsan sojojin kasar, Viktor Muzhenko sun gabatar da rahoto ga shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko, suna mai cewar, a yanzu biranen Artemovsk, da Druzhkovka dake yankin Donetsk da kuma biranen Kramatorsk da Konstantinovka suna karkashin ikon dakarun Ukraine.

Sun kuma shaidawa shugaban kasar matakin da aka dauka na tabbatar da doka da oda a gabashin Ukraine.

Shugaban kasar Ukraine shi kuma ya bayar da umurni da a mai da hankali wajen cire bama-bamai domin kare farar hula daga samun rauni, ya kuma bayar da umurnin kara gina wuraren inganta jin dadin rayuwar jama'a, tare da samar da abinci da ruwan sha, da kuma samar da taimakon agaji ga mazauna biranen.

Dakarun Ukraine sun kara kame birnin Slavyansk a ranar Asabar, a inda kuma nan take, suka fara maido da doka da oda a birnin.

To amma jamhuriyar jama'ar Donetsk sun tsaya a kan cewar, janyewar da suka yi ba wai yana nufin an murkushe rikicin ba ne. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China