Babban sakataren MDD Ban Ki-moon yana kan hanyarsa ta zuwa kasashen Rasha da Ukraine a kokarin da ake na lalubo bakin zaren warware rikicin kasar ta Ukraine cikin ruwan sanyi.
Kakakin Ban Ki-moon ya shaida wa manema labarai cewa, ana sa ran Mr. Ban zai yada zangonsa na farko a Moscow, inda zai gana da shugaba Vladimir Pitun, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov da sauran manyan jami'an kasar.
A ranar Jumma'a ne ake sa ran Ban ki-moon zai isa Kiev, babban birnin kasar Ukraine inda zai tattauna da mai rikon mukamin shugaban kasar Oleksandr Turchynov, firaministan kasar Arseniy Yatsenyuk da sauran jami'an kasar.
Bugu da kari, Mr. Ban zai gana da mambobin tawagar kare hakkin bil-adama ta MDD da wakilan kungiyoyin fararen hula da ke Kiev. (Ibrahim)