in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar Conmebol na neman sassauta hukuncin da aka yankewa Suarez
2014-07-11 16:24:15 cri
Shugaban hukumar kula da kwallon kafar nahiyar kudancin Amurka reshen kasar Uruguay Eugenio Figueredo, ya ce yanzu haka suna ci gaba da daukar matakan da suka wajaba, domin ganin an sassauta hukuncin da FIFA ta yankewa Luis Suarez, bayan da ta same shi da laifin cizon wani dan wasa, a daya daga wasannin da Uruguay din ta buga a gasar cin kofin duniya da ake yi yanzu haka.

Sashen hukunta laifuka na hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA dai ya dakatar da Suarez daga buga wasanni 9 ga kasar sa, tare da hana shi shiga duk wata hulda da ta shafi kwallon kafa har tsahon watanni 4, baya ga tarar dalar Amurka 112,000 da aka dora masa.

Game da hakan ne Figueredo ya ce yanzu haka suna iyakacin kokarin ganin an sassauta wannan hukunci, musamman ma batun yawan wasanni da aka hana Suarez bugawa.

A baya dai shuwagabannin hukumar kwallon kafar kasar ta Uruguay, sun zargi Figueredo da kin daukar wani mataki game da dakatar da Suarez.

A hannu guda kuma idan har waccan dakatarwa da aka yiwa Suarez ba ta sauya ba, dan wasan zai rasa damar buga wasannin da za a yi a gasar cin kofin kalubale na "America Cup" badi a kasar Chile, da kuma wasu wasanni na share fagen gasar cin kofin duniya na shekarar 2018.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China