Za a gudanar da taron tattalin arzikin Afirka na Fobes karo na 3 a Congo Brazzaville
Bisa labarin da jaridar Union ta kasar Gabon ta bayar a ranar 10 ga wata, an ce, za a bude taron tattaunawa kan tattalin arziki na Fobes karo na 3 a ranar 25 ga wata a kasar Congo Brazzaville, inda ake sa ran shugabannin kasashen Senegal, Afirka ta Kudu, Burkina Faso da tsohon babban sakataren MDD da kuma masanan tattalin arziki za su halarta.
Taken taron na wannan karo shi ne "adadin mutanen da suke mu'amala da banki".
A yayin taron, mahalartan za su yi nazari kan halin da ake ciki game da bunkasuwar bankunan nahiyar Afirka, tare da tattauna manufofin raya bankuna ta yadda za su dace da yankuna, da kuma sa kaimi ga yin kwaskwarima kan harkokin bankuna. (Zainab)