in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bunkasuwar kasashen da suka fi samun ci gaban tattalin arziki ta fuskanci tafiyar hawainiya
2014-06-11 15:16:29 cri
Bisa rahoton da kungiyar hadin kai da raya tattalin arziki ta duniya wato OECD ta gabatar a ranar 10 ga wata, an ce, bunkasuwar wasu muhimman kasashen da suka fi samun ci gaban tattalin arziki ta fuskanci tafiyar hawainiya, amma ana kokarin raya tattalin arziki a kasashe mambobin kungiyar OECD.

Rahoton ya bayyana cewa, alkaluman tattalin arzikin kasashe 5 na nahiyar Asiya wato Sin, Indiya, Koriya ta Kudu, Japan da kuma Indonesia ya ragu a kai a kai a cikin watanni biyar da suka gabata, wannan ya nuna cewa, bunkasuwar tattalin arzikinsu ta fuskanci tafiyar hawainiya.

Tun daga karshen shekarar 2013, har zuwa yanzu, cikakken alkaluman tattalin arziki ta kasashe mambobin OECD ta kiyaye 100.6, wannan ya bayyana cewa, an kiyaye karfin raya tattalin arziki a kasashen. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China