in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu za ta mai da hankali wajen kara farfado da tattalin arziki
2014-06-18 10:54:16 cri

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya ce, sabuwar gwamnatinsa za ta mai da hankali wajen habbakar tattalin arzikin kasar.

A yayin da yake jawabi game da halin da kasarsa ke ciki ga majalisar dokoki, wacce aka zaba a kasar a karo na biyar, Zuma, ya ce, samar da nagartaccen aiki shi ne babban makami na yaki da talauci, kuma hakan na bukatar kara kaimi wajen habbakar tattalin arziki.

Tuni dai har shugaban kasar ta Afrika ta Kudu, ya bayyana cewar, nan da shekara ta 2019, habbakar tattalin arzikin kasar zai kai kashi 5 bisa dari a ko wace shekara.

Zuma ya kara da cewa, kasar ta Afrika ta Kudu na bukatar mataki na gaggawa da zai zaburar da tattalin arzikin kasar, da zimmar murkushe talauci, da matsalar rashin aikin yi, da kuma banbancin matsayi na rayuwa.

Shugaba Zuma ya bayyana cewar, tattalin arzikin Afrika ta Kudu ya samu koma baya a shekaru ukku da suka shude, kuma wannan ya sa jama'ar kasar da yawa suna cikin wahala, ya danganta matsalar tafiyar hawainiya na tattalin arzikin kasar, da matsalar koma baya da aka samu na ci gaban tattalin arziki na duniya, da kuma matsaloli na cikin gidan kasar, wadanda suka hada da yajin aiki, wanda ke daukar tsawon lokaci, kuma a wani lokaci yana haifar da tashin hankali. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China