in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan riba da aka samu daga hannun jari da aka zuba a kasashen Afirka ya karu
2014-07-04 16:07:15 cri

Rahoto kan bunkasuwar tattalin arzikin Afirka na shekarar 2014 da aka bayar a yayin taron cinikayya da bunkasuwa na MDD a ranar 3 ga wata ya yi nuni da cewa, tun bayan da aka shiga karni na 21, yawan riba da aka samu daga hannun jari da aka zuba a nahiyar Afirka ya karu a bayyane, in an kwatanta da na karshen karnin da ya gabata.

Rahoton ya ce, a shekaru 90 na karnin da ya gabata, idan ana son samun wasu muradu, sai an bukaci a zuba jari na dala 7.4, amma a shekaru 10 na farkon wannan karni, in ana son cimma wadannan muradu, sai an bukaci zuba dala 4.1 kawai.. Sakamakon haka, ana ganin cewa, yawan riba da aka samu daga hannun jari da aka zuba a Afirka ya fi yawa sosai a kasashe masu tasowa da ke nahiyar Amurka, har ma ya fi yawa akasashe maso tasowa na Asiya.

Haka zakila rahoton ya , dalilan da suka janyo hakan su ne, kyautatuwar manyan ayyukan more rayuwar jama'a, da kyautatuwar hanyoyin samun fasahohin zamani, da yin gyare-gyare kan wasu manufofin da abin ya shafa. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China