in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Korea ta Kudu sun cimma ra'ayi daya a wasu sabbin fannoni a lokacin ziyarar shugaban kasar Sin a Korea ta Kudu
2014-07-04 21:10:19 cri

A ganin kasashen Sin da Korea ta Kudu, kasashen 2 sun cimma ra'ayi daya a wasu sabbin fannoni a lokacin ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a Korea ta Kudu, tabbas ziyarar shugaba Xi za ta bunkasa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 bisa manyan tsare-tsare, kamar yadda Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya fada yau Jumma'a 4 ga wata a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing.

Dangane da batun nukiliya a zirin Korea, Hong Lei ya ce, Sin da Korea ta Kudu sun cimma daidaito a fannoni 4, na farko, tabbatar da rashin kasancewar nukiliya a zirin Korea da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Korea sun dace da moriyar kasashe 6 da suka yi shawarwari kan batun nukiliya na zirin Korea ta, don haka ya kamata masu ruwa da tsaki su daidaita wadannan batutuwan da aka ambata a baya ta hanyar yin tattaunawa da shawarwari. Na biyu, ya kamata masu ruwa da tsaki su aiwatar da sanarwar hadin gwiwa da kudurorin da abin ya shafa a tsanake. Na uku, ya kamata masu ruwa da tsaki su ci gaba da sa kaimi kan gudanar da shawarwarin tare da inganta tuntubar juna da daidaitawa a tsakanin juna. Na hudu, ya kamata masu ruwa da tsaki su yi kokarin maido da yin shawarwarin. Har wa yau Sin da Korea ta Kudu sun goyi bayan shugabannin tawagogin wakilan da ke halartar shawarwarin da su tattauna ta hanyoyi daban daban, a kokarin ganin an samu ci gaba na a-zo-a-gani wajen tabbatar da rashin wanzuwar makaman nukiliya a zirin na Korea. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China