Haka kuma shugabannin biyu sun cimma daidaito kan fannoni daban daban, inda suka tsaida kudurin kara inganta dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, a kokarin samun bunkasuwa tare, da shimfida zaman lafiya a shiyya-shiyya tare, da farfado da Asiya tare, da kuma sa kaimi ga samun albarka a duk duniya baki daya.
A yammacin wannan rana, Madam Peng Liyuan, uwargidan shugaba Xi Jinping, ta kai ziyara a fadar Changdokkung da aka maida shi wurin adana kayayyakin al'adun gargajiya na tarihi da aka gada daga kaka da kakanni na duniya. A lokacin ziyarar, Madam Peng ta bayyana cewa, an dade ana sada zumunci tsakanin Sin da Koriya ta Kudu, don haka tana maraba da mutanen Koriya ta Kudu da ke sha'awar kawo ziyara. (Zainab)